Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Saratu Gidado 'Daso': Babu wata salon mugunta da ban iya ba kuma da aure na nake yin fim- cewar Saratu Daso

Babu wata salon mugunta da ban iya ba kuma da aure na nake yin fim- cewar Saratu Daso

A cewar ta tana tsare mutuncin aurenta kuma tana fim kamar yadda sauran mata ke tafiyar da aikin su a ma'aikata da dama da ma masu aikin sana'ar hannu.

Sanannen jaruma Saratu Gidado wanda aka fi sani da Daso ta sanar cewa da aurenta take yin fim  kuma mijinta yana sane da irin matsayin da take fitowa a cikin shirin fim.

Fitacciyar jaruma wanda ta fiye fitowa a matsayin muguwa ko mai azabtarwa a cikin fina-finai hausa Saratu Gidado ta shaida ma wakilin bbchausa cewa da mijinta yana mara mata bisa aikin fadarkarwa da yan fim keyi kuma bata taba nadamar aikin da take yi.

*Tsohuwar jarumar Kannywood tace ta samu duk wani nasara da take nema yayin da take fim

Matsayin hada aure da yin fim

A cewar ta tana tsare mutuncin aurenta kuma tana fim kamar yadda sauran mata ke tafiyar da aikin su a ma'aikata da dama da ma masu aikin sana'ar hannu.

"Ni matar aure ce, miji na ya barni ina cigaba da harkar fim, da yake a hanyar fim Allah ya hada mu kuma muka yi auren mu. Saboda haka ina cigaba da aiki na kamar yadda matar aure take aikin asibiti, matar aure take koyawa a makarantu, matan aure suke aikin gwamnati, matan aure suke siyasa, matan aure ke duk wata sana'a dake kawo masu kobo cikin rufin asiri. Ni dai ina kiyaye mutuncin aure na.  inji jarumar.

A cewarta mai gidan ta baya jin komai ganin yanayin rawan da take takawa a fim na fitowa a matsayin mugunta domin ya san cewa wasan kwaikwayo ne.

*“Ba harkar fim kadai ke gabana” - inji jaruma

Yawan fitowarta a matsayin muguwa

Jarumar wanda aka fi kira da Saratu daso tace babu wani salon mugunta da bata iya ba amma a cikin fim domin a zahiri ita ba mai wannan halin bane.

"Ni ba muguwa bace, ni mai kirki ce a zahiri. Bani da son magana a fili ma."tace.

Daso ta tsunduma cikin harkar fim inda ta kwashi kusan shekaru 18 tana harkar.

*Hanyar da za'a bi domin samun cigaba a masana'antar kannywood

Sai dai yanzu jarumar tace lokaci yayi da zata ringa fitowa a cikin natsuwa domin a yanzu ba zata iya fitowa tana mai zura gudu ko kuma mai ihu tana tafiya.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments