Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Yan matan Dapchi: Fadar shugaban kasa ta tabbatar da dawowar yan matan da aka sace

Shugaba Buhari ya gana da iyayen yan matan da aka sace

An dawo da yan matan ne a daidai inda aka sace su a garin Dapchi safiyar ranar Laraba

Fadar shugaban kasa tayi karin haske kan labarin dawowar yan matan Dapchi da yan  ta'adasuka sace.

A wata labari da aka fitar, mayakan boko haram sun dawo da yan matan garin Dapchi daidai inda suka sace su cikin motocin su a safiyar ranar laraba 21 ga wata.

Mai yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari hidima kan yadda labarai Bashir Ahmad ya tabbatar da dawowar su inda ya kara da cewa dawowar su ya nuna cewa shugaban kasa ya cika alkawarin da ya dauka ga iyayen matan.

"Labari mai dadi, Muna yi Allah godiya dawowar yan uwan mu cikin koshin lafiya. Alhamdulillah" ya rubuta a shafin sa na twitter.

Ya kuma bayyana alkawarin da shugaban ya dauka ga iyayen matan yayin da ya kai masu ziyara.

"Yanzu haka yan matan suna hannun hukumar DSS a nan garin Dapchi kuma nan bada dadewa za'a yi bayani ga jama'a kan lamarin" ya kara.

Sai dai an samu samu ragoyar mata biyar daga yan mata 110 da aka sace. Sun rasu a hannun yan ta'adda



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments