Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Da dumi-dumi: Arsene Wenger, kociyar kungiyar Arsenal yayi murabus

Arsene Wenger

Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar

Shaharren mai horas da tawagar kungiyar kwallo ta Arsenl wato  Arsene Wenger yayi ta maza, yayi murabus.

Kociyar ya kwashi tsawon shekaru 22  yana horas da sannanen kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila.

Zai bar kungiyar ne a karshen kakar bana kamar yadda ya sanar a wata takarda da ya fitar ma kungiyar.

Kamar yadda labarin ya fito a shafin kungiyar ta yanar gizo, Arsene Wenger yana ma kungiyar da dinbim magoya bayan ta dake ko'ina a fadin duniya godiya game da damar da aka bashi na jagorantar tawagar yan wasan ta na tsawon shekaru 22.

Dan kasar faransa mai shekaru 63, shine kociya mafi dadewa a tamaular firimiya na Ingila kuma yayi nasarar horar da Arsenal a wassanni 823.

Yayi murabus ne kafin karewar kwantiragin sa wanda sai cikin kakar badi zai kawo karshe.

 



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments