Main Logo

Main Logo
LexxyTech Corporation

Zargin wawure kudin jiha: Atiku da jiga-jigan PDP sun kaima tsohon gwaman ziyara a gidan yari

EFCC ta kama Jonah Jang bisa zargin da take masa na yin badakala da kudin jiha

Tsohon gwamnan kuma dan majalisar dattawa yana tsare ne a gidan yari bisa karar da EFCC ta shigar kan laifin wawushe kudin jiha

Tsohonn mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakara tare da wasu yayan jam'oyar PDP sun kaima tsohon gwamna, Jonah Jang wanda ke tsare a gidan yari ziyara.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, tsohon mataimakin shugaban kasa wanda aka sa ran cewa zai fito takarar kujerfar shugaban kasa a zaben nan gaba, ya ziyarcin gidan yarin tare da Farfesa Jerry Gana da wasu kusoshi jam'iyar PDP.

Hukuncin kotu

Tsohon gwamnan jihar Filato, yana tsare ne a gidan kaso bayan damar da kotu ta bada na a cigaba da tsaron shi.

Kotun ta bada umarnin cigaba da tsaran shi har zuwa ranar 24 ga watan Mayu bisa karar laifin wawure kudin jihar da aka shigar.

A zaman kotu da aka yi ranar laraba 16 ga wata, alkali Daniel Longji ya ki amincewa da bukatar belin da tsohon gwamnan ya nema. Daga ranar zantar da hukunci har sai bayan ya gama nazari kan karar shi.

Zargin da EFCC take masa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da karar inda take zargin tsohon gwamnan da yin sama da fadi da makuden kudin jihar har Nera biliyan shida da miliyan dubu uku.

Hukumar EFCC tana tuhumar Jonah Jang da wawure Nera 6.3bn daga cikin zargin laifuka 12 da take yi masa da suka hada da almubazaranci da karkata kudin jama'a, cin amana da rashin gaskiya amma ya musanta dukansu.



from pulse.ng - Nigeria's entertainment & lifestyle platform online

Post a Comment

0 Comments